عن هانئ مولى عثمان قال: كان عثمان إذا وقف على قبر بَكى حتى يَبُلَّ لحيته، فقيل له: تَذْكُر الجنة والنار فلا تَبكي وتبكي مِن هذا؟ فقال: إن رسول الله - صلى الله عليه وسلم- قال: «إنَّ القبرَ أولُ مَنْزِل من منازل الآخرة، فإنْ نجا منه فما بعده أيسر منه، وإنْ لم ينجُ منه فما بعده أشد منه».
[حسن] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد]
المزيــد ...
An rawaito daga Hani Maula Usman ya ce: Usman ya kasance idan ya tsaya kan Qabari yakanyi kuka har ya jiqa gemunsa, sai aka ce da shi: kana tuna Aljanna da Wuta baka yin kuka amma kuma kayi kuka da wannan? sai ya ce: lallai manzon Allah SAW ya ce: "Lallai Qabari shi ne farkon Masauki daga cikin Masaukan Lahira, to idan Mutum ya tsira a cikinsa to babu abunda yafi sauqi kamar abu nagabansa, kuma idan bai tsira ba acikinsa to babu abunda ya fi shi tsanani"
[Hasan ne] - [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]
Usman Bn Affan -Allah ya yarda da shi- ya kasance idan ya tsaya akan Kabari yankanyi Kuka har Gemunsa ya jiqe, sai aka ce da shi:kana tuna Aljanna da Wuta baka kuka amma kana kuka a Qabari? sai ya basu labarin cewa yaji Manzon Allah SAW yana bada Labari cewa Lallai Qabari shi ne farkon Masauki daga cikin Masaukan Lahira, to idan Mutum ya tsira a cikinsa to babu abunda yafi sauqi kamar abu nagabansa, kuma idan bai tsira ba acikinsa to babu abunda ya fi shi tsanani; Saboda idan yana da Zunubi to za'a kankare masa shi da da Azabar Qabari, in kuwa bai tsira ba a cikinsa, daga Azaba ko kuma a kankare masa Zunubansa da shi ya wanzu kan wani abu aknasa da ya cancanci Azaba to babu mafi tsanani kamar abunda yaje bayansa, Saboda Azabar Wuta ita ce Mafi tsanani