kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu, sai ya ce: "@Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci*" Sannan ya dauki wani danyan itacan dabino, sai ya raba shi biyu, sai ya kafa daya a kowanne kabari, suka ce: Ya Manzon Allah, meyasa ka aikata hakan, sai ya ce: "Watakila a saukaka musu muddin dai basu bushe ba".
عربي Turanci urdu
«Lallai ƙabari shi ne farkon masauki daga masaukan Lahira, idan mutum ya tsira a cikinsa to abinda ke bayansa ya fishi sauƙi, idan kuma bai tsira a cikinsa ba to abinda ke bayansa ya fi shi tsanani».
عربي Turanci urdu