Karkasawa:
+ -
عن عبدِ الله بن عمرو رضي الله عنهما قال:

كنتُ أكتبُ كلَّ شيءٍ أسمعُه من رسولِ الله صلَّى الله عليه وسلم أُريدُ حفْظَه، فنهتْني قريشٌ، وقالوا: أتكْتبُ كلَّ شيءٍ تَسمَعُه من رسول الله صلَّى الله عليه وسلم، ورسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم بَشَرٌ يتكلَّمُ في الغضَبِ والرِّضا؟ فأمسَكتُ عن الكتاب، فذكرتُ ذلك لرسول الله صلَّى الله عليه وسلم، فأومأ بإصبَعِه إلى فيه، فقال: «اكتُبْ، فوالذي نفسي بيدِه، ما يَخرُجُ منه إلا حقٌّ».
[صحيح] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 3646]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Na kasance ina rubuta dukkan abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son haddace shi, sai Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Shin ka dinga rubuta dukkan abin da ka ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, alhali Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin fushi da yarda? sai na dakata daga rubutun, sai na fadawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hakan sai ya yi nuni da 'yan yatsunsa zuwa bakinsa, sai ya ce: "Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya".

[Ingantacce ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 3646]

Bayani

Abdullah ɗan Amr - Allah Ya yarada da su - ya ce: Na kasance ina rubuta dukkanin abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - don na haddace shi a rubuce, sai wasu mutane daga Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin yarda da fushi, zai iya yin kuskure, sai na daina rubutun.
Sai na ba wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - labarin abin da suka faɗa, sai ya yi nuni da danyatsansa zuwa bakinsa, sai ya ce; Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da yake fita daga cikinsa sai gaskiya a kowanne hali, haka a halin yarda da fushi.
Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa game da AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Ba ya magana bisa son rai* shi (Alƙur'ani) ba wani abu ba ne ba ban da wahayi da ake saukar masa) [Al-najm 3-4].

الملاحظة
تفسير الايه الكريمه في قوله (ماينطق عن الهوي) :-حيث لايتكلم بهواه من ماترى نفسه (إن هو إلا وحي يوحى) بل يتحدث بنقله وحى الله له إليكم *إسناد لمقولة متواترة سمعتها عند بعض اهل العلم انه منع الرسول صحابته أن يكتبو عنه شي غير كلام الله وتفسيره
النص المقترح قال عبدُ الله بن عَمْرو رضي الله عنه: كنتُ أكتبُ كلَّ شيءٍ أسمعه مِن رسول الله صلى الله عليه وسلم لكي أحفَظَه بالكتابة، فنهاني رجالٌ من قريش، وقالوا: رسولُ الله صلى الله عليه وسلم بشرٌ يتكلَّم في الرِّضا والغضب، وقد يُخطئ، فتوقَّفت عن الكتابة. فأخبرتُ النبيَّ صلى الله عليه وسلم بما قالوه، فأشار بإصبعه إلى فَمِهِ فقال: اكتب، فوالذي نفسي بيده ما يَخرجُ منه إلّا حقّ على كل حال، وفي الرِّضا والغضب. وقد قال تعالى عن نبيه صلى الله عليه وسلم: ﴿وَمَا یَنطِقُ عَنِ ٱلۡهَوَىٰۤ * إِنۡ هُوَ إِلَّا وَحۡیࣱ یُوحَىٰ﴾ [النجم ٣-٤].

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ma'asumi (wanda ba ya laifi, kuma ba ya kuskure) ne a cikin abin da yake isar da shi daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - a halin yarda da fushi.
  2. Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - a kan kiyaye sunna da isar da ita.
  3. Halaccin rantsuwa ko da ba a sa a yi rantsuwar ba don maslaha, kamar ƙarfafa wani al'amari.
  4. Rubuta ilimi yana daga mafi muhimmancin dalilai da suke kiyaye ilimi.
Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin
kashe kashe
Kari