Karkasawa:
عَن أَبي مُوْسى الأَشْعريِّ رضي الله عنه قال: قال رسولُ اللهِ صلى اللهُ عليه وسلم:

«مَثَلُ الْمُؤْمِنِ الَّذِي يَقْرَأُ الْقُرْآنَ كَمَثَلِ الْأُتْرُجَّةِ، رِيحُهَا طَيِّبٌ وَطَعْمُهَا طَيِّبٌ، وَمَثَلُ الْمُؤْمِنِ الَّذِي لَا يَقْرَأُ الْقُرْآنَ كَمَثَلِ التَّمْرَةِ، لَا رِيحَ لَهَا وَطَعْمُهَا حُلْوٌ، وَمَثَلُ الْمُنَافِقِ الَّذِي يَقْرَأُ الْقُرْآنَ مَثَلُ الرَّيْحَانَةِ، رِيحُهَا طَيِّبٌ وَطَعْمُهَا مُرٌّ، وَمَثَلُ الْمُنَافِقِ الَّذِي لَا يَقْرَأُ الْقُرْآنَ كَمَثَلِ الْحَنْظَلَةِ، لَيْسَ لَهَا رِيحٌ وَطَعْمُهَا مُرٌّ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kwatankwacin muminin da yake karanta AlKur'ani kamar gawasa ne, kanshinta mai dadi ne, kuma dandanonta mai dadi ne, kuma kwatankwacin muminin da ba ya karanta AlKur'ani kamar dabino ne ba shi da kanshi amma dandanonsa ma zaki ne, kuma kwatankwacin munafikin da yake karanta AlKurani kamar nana ne kanshinsa mai dadi ne amma dandanonta mai daci ne, kuma kwatankawacin munafikin da ba ya karanta AlKura'ni kwatankwacin guna ce ba ta da kanshi, kuma dandanonta mai daci ne".

الملاحظة
هذه ترجمة حديث مثل المؤمن الذي يقرأ القرآن إلى لغة الهوسا. "Daga Abu Musal Al-Ash'ariy, shi kuma daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, Manzon Allah ya ce: "Misalin Mumini wanda yake karanta Alƙur'ani kamar misalin lemun zaƙi ne, ƙamshin sa yana da daɗi, hakanan ma ɗanɗanon sa, shi kuma misalin muminin da ba ya karatun Alƙur'ani kamar misalin Dabino ne, Dabino ba ya da ƙamshi, amma ɗanɗanon sa yana da zaƙi, shi kuwa misalin Munafuki, wanda ba ya karatun Alƙur'ani kamar misalin kwartowa ce, Ita kwartowa ba ta da ƙamshi, amma ɗanɗanon ta yana da matuƙar ɗaci" (Bukhariy da Muslim suka rawaito shi)
النص المقترح عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مثَلُ المؤمن الذي يقرأ القرآن مَثَلُ الأُتْرُجَّةِ: ريحها طيب وطعمها طيب، ومَثَل المؤمن الذي لا يقرأ القرآن كمَثَلِ التمرة: لا ريح لها وطعمها حُلْوٌ، وَمَثل المنافق الذي يقرأ القرآن كمثل الريحانَة: ريحها طيب وطعمها مُرٌّ، وَمَثَل المنافق الذي لا يقرأ القرآن كمثل الحَنْظَلَةِ: ليس لها ريح وطعمها مُرٌّ».
الملاحظة
جيد
النص المقترح عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مثَلُ المؤمن الذي يقرأ القرآن مَثَلُ الأُتْرُجَّةِ: ريحها طيب وطعمها طيب، ومَثَل المؤمن الذي لا يقرأ القرآن كمَثَلِ التمرة: لا ريح لها وطعمها حُلْوٌ، وَمَثل المنافق الذي يقرأ القرآن كمثل الريحانَة: ريحها طيب وطعمها مُرٌّ، وَمَثَل المنافق الذي لا يقرأ القرآن كمثل الحَنْظَلَةِ: ليس لها ريح وطعمها مُرٌّ».
الملاحظة
جتكعبهبهقخلخفخل
النص المقترح متبامعبببپببب ما سي هبهل

Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana karkasuwar mutane a karatun AlKur'ani da amfanuwa da shi:
Kashi na farko: Muminin da yake karanta AlKur'ani kuma yake amfanuwa da shi, to shi kamar gawasa ne, mai dadin dandano da kanshi, da kyakkyawan launi, kuma amfaninsa mai yawa ne, shi yana aiki da abinda ya karanta, kuma yana amfanar bayin Allah.
Kashi na biyu: Muminin da ba ya karanta AlKur'ani, to shi kamar dabino ne, dandanonsa mai zaki ne, kuma ba shi da kanshi, to zuciyarsa mai tattare da imani ce kamar tattarowar dabino akan zaki a dandanonsa da cikinsa, da rashin bayyanar kanshi gare shi wanda mutane za su shaka; Saboda rashin bayyanar karatu daga gare shi wanda mutane za su ji dadin jinsa.
Na uku: Munafikin da yake karanta AlKur'ani: To shi kamar nana ne, tana da dadin kanshi kuma dandanonta mai daci ne, ta inda bai gyara zuciyarsa da imani ba, kuma bai yi aiki da AlKur'ani ba, kuma yana bayyana ga mutane cewa shi muminine, to kanshinta mai dadi yana kama da karatunsa, dandanonta mai daci kuma yana kama da kafircinsa.
Na hudu: Munafikin da ba ya karanta AlKur'ani, to shi kamar guna ne, ta inda ita ba ta da kanshi, da kuma dacin dandanonta, to rashin kanshinta ya yi kama da rashin kanshinsa; Saboda rashin karatunsa, kuma dacin dandanonta ya yi kama da dacin kafircinsa, cikinsa ya kadaita daga imani, zahirinsa kuma babu amfani a cikinsa, kai shi mai cutarwa ne.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Ma"anonin Kalmomi

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin falalar mai dauke da AlKur'ani mai aiki da shi.
  2. Daga hanyoyin koyarwa akwai buga misalai; Dan kusanto da fahimta.
  3. Yana kamata ga musulmi ya zama yana da wani wuridai da yake yi kullum na karatun littafin Allah - Madaukakin sarki -.
kashe kashe
Kari