عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رضيَ اللهُ عنهما:
أنَّهُ قَالَ لعَطَاءِ بْنِ أَبِي رَبَاحٍ: أَلَا أُرِيكَ امْرَأَةً مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ؟ قُلْتُ: بَلَى، قَالَ: هَذِهِ الْمَرْأَةُ السَّوْدَاءُ، أَتَتِ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَتْ: إِنِّي أُصْرَعُ وَإِنِّي أَتَكَشَّفُ، فَادْعُ اللهَ لِي، قَالَ: «إِنْ شِئْتِ صَبَرْتِ وَلَكِ الْجَنَّةُ، وَإِنْ شِئْتِ دَعَوْتُ اللهَ أَنْ يُعَافِيَكِ» قَالَتْ: أَصْبِرُ، قَالَتْ: فَإِنِّي أَتَكَشَّفُ فَادْعُ اللهَ أَنْ لَا أَتَكَشَّفَ، فَدَعَا لَهَا.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2576]
المزيــد ...
Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su:
Cewa shi ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah; Shin bana nuna maka wata mace daga cikin 'yan aljanna ba? na ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar da ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Ni ina farfaɗiya kuma inayin tsirara, to ka roƙamin Allah, ya ce: «Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki» ta ce: Zan yi haƙuri, ta ce : To cewa inayin tsirara to ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara, sai ya roƙa mata.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2576]
Ibnu Abbas - Allah Ya yarda dasu - ya cewa Aɗa'u ɗan Abi Rabah: Shin bana nuna maka wata mata daga cikin 'yan aljanna ba? Aɗa'u ya ce: Eh, ya ce: Wannan baƙar matar mutuniyar Habasha, ta zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta ce: Lallai cewa ni ina da cutar farfaɗiya kuma cewa ni ina yin tsirara wani abu yana yayewa daga jikina alhali ni ban sani ba, to ka roƙamin Allah Ya yaye mini, ya ce: Idan kin so ki yi haƙuri aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so zan roƙa miki Allah Ya yaye miki, ta ce: To zan yi haƙurin, sannan ta ce: To ka roƙamin Allah kada in sake yin tsirara idan na yi farfaɗiya, sai ya roƙa mata Allah.