عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«الْمَاهِرُ بِالْقُرْآنِ مَعَ السَّفَرَةِ الْكِرَامِ الْبَرَرَةِ، وَالَّذِي يَقْرَأُ الْقُرْآنَ وَيَتَتَعْتَعُ فِيهِ، وَهُوَ عَلَيْهِ شَاقٌّ، لَهُ أَجْرَانِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 798]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Gangaran a karatun Alƙur'ani yana tare da manyan mala'iku masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karanta Alƙur'ani kuma yake guragura a cikinsa yana mai shan wuya to yana da lada biyu.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 798]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda yake karanta Alƙur'ani, alhali shi mai kyakkyawar hadda ne mai kyautatawa, kuma gwani haziƙi a karanta shi, to a lahira yana da ladan da zai zama a matsayinsa tare da manyan mala'iku matafiya masu karamci. Kuma wanda yake karanta Alƙur'ani yake guragura a cikinsa yana kaikawo a karanta shi; dan raunin haddarsa alhali shi tare da hakan yana riƙe da shi, kuma yana wahalar da shi to shi yana da lada biyu; ladan karatun Alkur'ani da kuma ladan wahala da kaikawo a cikin karanta shi.