عن عائشةَ أمِّ المؤْمنِين رضي الله عنها قالت:
لَمْ يَكُنِ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى شَيْءٍ مِنَ النَّوَافِلِ أَشَدَّ مِنْهُ تَعَاهُدًا عَلَى رَكْعَتَيِ الفَجْرِ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1169]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce :
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimtar wani abu na nafiloli ba kamar raka'o'i biyu na Alfijr.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1169]
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance mafi tsananin lazimta da kuma kiyaye wa ba akan wani abu na nafiloli sama da raka'o'i biyu ratibai na kafin sallar Asuba ba.