+ -

عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رَضيَ اللهُ عنهُما:
أَنَّ أُمَّهُ بِنْتَ رَوَاحَةَ سَأَلَتْ أَبَاهُ بَعْضَ الْمَوْهِبَةِ مِنْ مَالِهِ لِابْنِهَا، فَالْتَوَى بِهَا سَنَةً ثُمَّ بَدَا لَهُ، فَقَالَتْ: لَا أَرْضَى حَتَّى تُشْهِدَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى مَا وَهَبْتَ لِابْنِي، فَأَخَذَ أَبِي بِيَدِي وَأَنَا يَوْمَئِذٍ غُلَامٌ، فَأَتَى رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّ أُمَّ هَذَا بِنْتَ رَوَاحَةَ أَعْجَبَهَا أَنْ أُشْهِدَكَ عَلَى الَّذِي وَهَبْتُ لِابْنِهَا، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا بَشِيرُ، أَلَكَ وَلَدٌ سِوَى هَذَا؟» قَالَ: نَعَمْ، فَقَالَ: «أَكُلَّهُمْ وَهَبْتَ لَهُ مِثْلَ هَذَا؟» قَالَ: لَا، قَالَ: «فَلَا تُشْهِدْنِي إِذن، فَإِنِّي لَا أَشْهَدُ عَلَى جَوْرٍ»، ولِمُسْلِمٍ: «فَأَشْهِدْ عَلَى هَذَا غَيْرِي».

[صحيح] - [متفق عليه، وله ألفاظ عديدة] - [صحيح مسلم: 1623]
المزيــد ...

Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su -:
Cewa mahaifiyarsa 'yar Rawaha ta tambayi babansa wata kyauta daga dukiyarsa ya bawa ɗanta, sai ya jinkirtata shekara sannan ya ga (ya kamata ya yi kyautar), sai ta ce: Ba zan yarda ba har sai ka sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi shaida ga abinda ka bawa ɗana kyauta, sai babana ya riƙe hannuna, a wannan lokacin ina yaro, sai ya zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa babar wannan 'yar Rawaha tana son in saka shaida a kan abinda na bawa ɗana kyauta, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya kai Bashir, shin kana da wani dan ne banda wannan?" ya ce: Eh, sai ya ce: "Shin dukkansu ka basu kwatankwacin wannan?" ya ce: A'a, ya ce: "To kada ka sani shaida, domin cewa ni bana yin shaida akan zalinci", A Muslim: "To kasa wani shaida akan wannan ba ni ba".

[Ingantacce ne] - - [صحيح مسلم - 1623]

Bayani

Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - ya bada labarin cewa mahaifiyarsa Amrah 'yar Rawaha - Allah Ya yarda da ita - ta tambayi babansa wata kyautar da zai bawa ɗanta daga dukiyarsa, sai ya yi nauyi ya jinkirtata har shekara, sannan ya ga ya kamata ya amsa mata abinda ta nema sai ya bawa ɗansa Nu'uman kyauta, sai ta ce: Ba zan yarda ba har sai ka sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sheda akan abinda ka bawa ɗana, sai babana ya riƙe hannuna ni kuma a wannan lokacin ina ƙaramin yaro, sai ya zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa babar wannan 'yar Rawaha tana son in sakaka shaida akan abinda na bawa ɗanta kyauta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ya kai Bashir, shin kana da wani ɗan ne banda wannan? Ya ce: Eh. Sai ya ce: Shin dukkansu ka ba su kwatankwacin wannan? Ya ce: A'a. Ya ce: To kada ka sa ni shaida, domin cewa ni ba na shaida a kan zalinci. A riwayar Muslim ya ce yana mai zarginsa: Sai dai ka sa wanina ya yi shaida a kan wannan zalincin.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wajabcin adalci tsakanin 'ya'ya maza da mata a bayar da kyauta, amma ciyarwa to ana ƙaddarata ne da buƙata kowa da gwargwadansa.
  2. Fifita wasu daga 'ya'ya akan wasu yana daga zalinci, kuma ɗaukar shaida ko bayar da ita ba ya halatta a cikinsa.
  3. Nawawi ya ce: Ya kamata ya daidaita tsakanin 'ya'yansa a kyauta, ya bawa kowane ɗaya irin abinda ya bawa ɗayan kada ya fifita, kuma ya daidaita tsakanin namiji da mace, wasu daga cikin malummanmu suka ce: A bawa namiji kwatankwacin rabon mata biyu, amma ingantaccen zancen da ya shahara shi ne ya daidaita tsakanisu saboda zahirin hadisin.
  4. Hukunce-hukuncen da suke faruwa akan saɓanin shari'a suna ɓaci kuma ba’a zartar da su.
  5. Alƙali da mai fatawa su yi bincike sosai daga abinda yake ɗaukar bincike; saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbbata agare shi -: "Shin ka yi wannan ga 'ya'yanka dukkansu?".
  6. Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa: Akwai halaccin maida kyautar uba ga ɗansa.
  7. Umarni da abinda yake sa soyayya tsakanin 'yan uwa, da barin abinda yake sa gaba ko yake haifar da saɓawa iyaye.