«مَنْ تَعَلَّقَ شيئا وُكِلَ إليه».
[ضعيف] - [رواه أحمد والترمذي] - [مسند أحمد: 18781]
المزيــد ...
An rawaito daga Abdullahi Bn Akim -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi "Duk wanda ya danfaru da wani abu to za'a jibanta shi zuwa gare shi"
Duk ya juyar da Zuciyarsa ko aikinsa ko baki dayansu zuwa wani abu da take kaunar Anfaninsa ko ije wata Cuta Allah zai jibanta shi zuwa wancan abun da ya rataya da shi, saboda duk wanda ya jibanta Al-amarinsa zuwa ga Allah to ya isar masa kuma zai sawwake masa kowa ne abu mai Wahala, kuma duk wanda ya jibanta al-amarinsa zuwa ga waninsa to Allah zai bar shi zuwa wancan abun kuma ya Kaskanta shi
خذلان من انصرف عن الله وطلب النفع من غيره.من تعلق بالله كفاه فهو القوي الذي بيده كل شيء ومن تعلق بغيره فإن ذلك الغير ضعيف لا يملك شيء