لَمَّا قَدِمَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الْمَدِينَةَ مِنْ غَزْوَةِ تَبُوكَ تَلَقَّاهُ النَّاسُ، فَلَقِيتُهُ مَعَ الصِّبْيَانِ عَلَى ثَنِيَّةِ الْوَدَاعِ.
[صحيح] - [رواه البخاري وأبو داود] - [سنن أبي داود: 2779]
المزيــد ...
An rawaito daga Al-Sa'ib Bn Yazid -Allah ya yarda da shi- yace: "Yayin da Annabi SAW ya iso Madina- daga yakin Tabuka Mutane sun tare sai na tare shi tare da Yara, kuma a cikin wata Riwayar ya ce:"Mun tafi mu taro Annabi SAW tare da Yara a Thaniyat Al-Wadaa"
[Ingantacce ne duka Riwayoyin nasa guda biyun] - [Buhari ne ya rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi]
Al-Sa'ib ya bada Labarin cewa shi yayin da Annabi ya SAW ya iso Madina tare da Sahabbansa suna masu dawowa daga yakin Tabuka sun futo don tarbarsu a Thaniyat Al-wadaa, kuma ita wani guri ne daf da Madina, kuma wannan don dauke musu kewa ne da dadada musu, da kuma kwadaitarwa ga wadanda basu futa yakin ba