+ -

عن رويفع قال: قال لي رسول الله صلى الله عليه وسلم : "يا رُوَيْفِعُ، لعل الحياة ستطول بك فأخبر الناس أن من عَقَدَ لِحْيَتَهُ، أو تَقَلَّدَ وَتَرًا، أو اسْتَنْجَى برَجِيعِ دابة أو عَظْمٍ، فإن محمدًا بريءٌ منه".
[صحيح] - [رواه أبو داود والنسائي وأحمد]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

Daga Ruwaifi'a ya ce: Manzon Allah ya ce da ni: "Ya kai Ruwaifia,watakila rayuwarka tayi tsawo, saboda haka bawa Mutane labarin cewa duk wanda ya daure gemunsa, ko ya daura tsirkiya, ko yayi tsarki turoson dabbobi ko kashi, to babu shi babu Annabi Muhammad
[Ingantacce ne] - [Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]

Bayani

Manzon Allah SAW- yana cewa wannan sahabin zai yi tsawon rai har sai ya fahimci mutanen da suka saba wa koyarwarsa - SAW- a cikin gemun da ke samar da shi da kuma girmama shi zuwa wasa da ita , ta Hanyar da zasu rika kamanceceniya da Baubaye ko ma'abota wasa ko Ma'abota kece raini da Dukiya da kuma karairaya kuma suna keta akidar tauhidi ta hanyar amfani da hanyoyin shirka, kuma suna sanya abun wuya ko suna sanyawa Dabbobinsui, kuma suna neman amfani da haramtattun abubuwa. Ko kuma su aikata abin da annabinsu ya hana su na yin tsarki da kashin Dabbobi. Annabi -SAW- ya yi Wasiyya ga sahabinsa da su isar ga Alumma cewa annabin nata ba ruwansa da wadanda yayi wani abu daga hakan.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin