عن عبد الله بنِ عمر رضي الله عنهما أن عمرَ بْن الخطاب رضي الله عنه قال: ((يا رسول الله، أّيَرقُدُ أَحَدُنا وهو جُنُب؟ قال: نعم، إِذَا تَوَضَّأ أَحَدُكُم فَليَرقُد)).
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Umar Allah ya yarda dasu Umar Dan Khaddab Allah ya yarda da shi yace: [Ya Manzon Allah, waninmu zai iya kwanciya da janaba? sai yace: E, zai iya, amma in yayi alwala
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
An tambayi Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- ya tambayi Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi: Idan janaba ta sami wani tun farkon dare ta hanyar saduwa da iyali ko mafarki, shi zai iya kwanciya bacci a haka? sai Mai tsira da amincin Allah ya basu damar yin haka amma idan anyi alwalla irin ta salla.