+ -

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما «أن رسول الله - صلى الله عليه وسلم - اصْطَنَعَ خَاتَمًا من ذهب، فكان يجعل فَصَّهُ في باطن كَفِّهِ إذا لَبِسَهُ، فصنع الناس كذلك، ثم إنه جلس على المنبر فَنَزَعَهُ فقال: إني كنت أَلْبَسُ هذا الخَاتَمَ ، وأجعل فَصَّهُ من داخل، فرمى به ثم قال: والله لا أَلْبَسُهُ أبدا فَنَبَذَ الناس خَواتِيمَهُمْ». وفي لفظ «جعله في يده اليمنى».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

An karbo daga Abdullahi Dan Umar-Allah ya yarda dasu-"Cewa Manzan Allah-tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi-yayi Zobe na Zinare,ya kasance idan zai sashi yana sanya kansa acikin tafinsa,sai Mutane sukai hakan,sannan cewa ya zauna akan Minbari sai ya cireshi yace:Hakika na kasance ina sanya wannan Zoben,kuma ina sanya kansa daga ciki,sai ya yar dashi sannan yace:Na rantse da Allah bazan kara sashi ba har abada sai Mutane suka jefar da Zobunansu".A wani Lafazin"Ya sanya shi a Hannunsa na Dama".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Annabi tshira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Umarni ai masa Zoben Dinare,ya kasance idan zai sashi yana sanya kansa cikin Tafinsa,sai Sahabbai suka bishi akan haka sukayi kamar yadda yayi,sannan bayan wani Lokaci Annabi tshira da Amincin Allah su tabbata agareshi ya zauna kan Minbari don Mutane su ganshi,sannan yace:Hakika na kasance ina sanya wannan Zoben,kuma ina sanya kansa acikin Tafina,sannan ya yarda shi yace:Na rantse da Allah bazan kara sashiba har abada,wannan ya faru ne bayan an haramtashi,sai Sahabbai suka jefar da Zobunansu saboda koyi da Manzan Allah tshira da amincin Allah su tabbata agareshi

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam
Manufofin Fassarorin