عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «لا يَمُوتُ لأحَدٍ من المسلمين ثلاثة من الوَلَد فتَمسُّه النَّار إلا تَحِلَّة القَسَم».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira =Allah ya yarda da shi- ya ce Manzon Allah SAW ya ce: "Babu wani Mutum daga cikin Musulmai da 'Ya'yansa uku zasu Mutu sannan kuma wuta ta tava shi sai karayar rantsuwa"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Idan mutum yaransa maza guda uku ko kuma mata biyu Suka Mutu kadai, ko kuma maza da mata, to, Allah - Madaukaki - ya haramta jikinsa cin wuta, idan ya yi hakuri, kuma ya nemi ladan Allah, kuma ya gamsu da hukuncin Allah Madaukakin Sarki ya Hukunta, da da Kaddararsa wacce take kubutar da Rantsuwa, ga wanda yake ketare Siraxi. Domin Allah Madaukaki yana cewa: (Kuma babu wani daga cikinku face sai ya ketare ta)