+ -

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيَّ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ:
بَعَثَ عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنَ اليَمَنِ بِذُهَيْبَةٍ فِي أَدِيمٍ مَقْرُوظٍ، لَمْ تُحَصَّلْ مِنْ تُرَابِهَا، قَالَ: فَقَسَمَهَا بَيْنَ أَرْبَعَةِ نَفَرٍ، بَيْنَ عُيَيْنَةَ بْنِ بَدْرٍ وَأَقْرَعَ بْنِ حابِسٍ وَزَيْدِ الخَيْلِ، وَالرَّابِعُ: إِمَّا عَلْقَمَةُ وَإِمَّا عَامِرُ بْنُ الطُّفَيْلِ، فَقَالَ رَجُلٌ مِنْ أَصْحَابِهِ: كُنَّا نَحْنُ أَحَقَّ بِهَذَا مِنْ هَؤُلاَءِ، قَالَ: فَبَلَغَ ذَلِكَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: «أَلاَ تَأْمَنُونِي وَأَنَا أَمِينُ مَنْ فِي السَّمَاءِ، يَأْتِينِي خَبَرُ السَّمَاءِ صَبَاحًا وَمَسَاءً»، قَالَ: فَقَامَ رَجُلٌ غَائِرُ العَيْنَيْنِ، مُشْرِفُ الوَجْنَتَيْنِ، نَاشِزُ الجَبْهَةِ، كَثُّ اللِّحْيَةِ، مَحْلُوقُ الرَّأْسِ، مُشَمَّرُ الإِزَارِ، فَقَالَ يَا رَسُولَ اللَّهِ اتَّقِ اللَّهَ، قَالَ: «وَيْلَكَ، أَوَلَسْتُ أَحَقَّ أَهْلِ الأَرْضِ أَنْ يَتَّقِيَ اللَّهَ» قَالَ: ثُمَّ وَلَّى الرَّجُلُ، قَالَ خَالِدُ بْنُ الوَلِيدِ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَلاَ أَضْرِبُ عُنُقَهُ؟ قَالَ: «لاَ، لَعَلَّهُ أَنْ يَكُونَ يُصَلِّي» فَقَالَ خَالِدٌ: وَكَمْ مِنْ مُصَلٍّ يَقُولُ بِلِسَانِهِ مَا لَيْسَ فِي قَلْبِهِ، قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنِّي لَمْ أُومَرْ أَنْ أَنْقُبَ عَنْ قُلُوبِ النَّاسِ وَلاَ أَشُقَّ بُطُونَهُمْ» قَالَ: ثُمَّ نَظَرَ إِلَيْهِ وَهُوَ مُقَفٍّ، فَقَالَ: «إِنَّهُ يَخْرُجُ مِنْ ضِئْضِئِ هَذَا قَوْمٌ يَتْلُونَ كِتَابَ اللَّهِ رَطْبًا، لاَ يُجَاوِزُ حَنَاجِرَهُمْ، يَمْرُقُونَ مِنَ الدِّينِ كَمَا يَمْرُقُ السَّهْمُ مِنَ الرَّمِيَّةِ»، وَأَظُنُّهُ قَالَ: «لَئِنْ أَدْرَكْتُهُمْ لَأَقْتُلَنَّهُمْ قَتْلَ ثَمُودَ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4351]
المزيــد ...

Daga Abu Sa'idul Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya aikewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani gutsire na zinare a cikin wata fatar da aka jeme da ƙwallan bagaruwa, ba'a gama tace shi daga ƙasarta ba, ya ce: sai ya raba shi tsakanin mutum huɗu, tsakanin Uyaina ɗan Badr da Aƙra'a ɗan Habis da Zaidul Khail, na huɗun: Ko dai Alƙama ko Amir ɗan Ɗufail, sai wani mutum daga sahabbansa ya ce: Mu mun kasance mu ne mafi cancantar wannan daga waɗannan (mutane huɗun), ya ce: Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «Shin bakwa amince mini ba alhali ni ne amintaccen wanda ke sama, labarin sama yana zo mini safiya da yamma", ya ce: Sai wani mutum ya mike mai kogon idanuwa, mai manyan kumatu, goshin shi ya yi sama, mai kaurin gemu, mai askakken kai, yana ɗaure da zani, sai ya ce: Ya Manzon Allah ka ji tsoron Allah, ya ce: "Kaicanka, shin ba ni ne nafi cancantar fin kowa tsoron Allah daga mutanen dake ƙasa ba" ya ce: Sannan mutumin ya juya baya, Khalid dan Walida ya ce: Ya Manzon Allah, shin bana daki wuyansa ba? ya ce: "A'a, wataƙila yana sallah" Khalid ya ce: da yawa mai sallar da yake faɗa da harshensa abinda ba ya cikin zuciyarsa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya ce: "Lallai ni ba'a umarceni ba in bibiyi zukatan mutane ba ko na tsaga cikkunansu ba" ya ce: sannan ya yi duba zuwa gare shi alhali shi ya juya baya, sai ya ce: "Lallai cewa wasu mutane zasu fito daga tsatson wannan suna karanta Littafin Allah danye a zuciyarsu, ba ya ketare zukatansu zasu fita daga Addini kamar yadda kibiya take fita ga kwarin da aka harba, ina zatan ya ce: Wallahi idan na riskesu zan kashesu irin kisan Samudawa.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4351]

Bayani

Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya yi aike zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Yaman da wani gutsire na zinari a cikin wata fata da aka jemeta da bagaruwa, gutsiren zinaren ba’a gama wanke shi daga ƙasarsa ba, ya ce: Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya rarraba shi tsakanin mutum huɗu: Uyaina ɗan Badr al-Fuzari, da Aƙra'a ɗan Habis al-Hanzali, da Zaidul Khail al-Nabahani, da Alƙama ɗan Alasa al-Amiri, sai wani mutum daga sahabbansa ya ce: Mune mafi cancanta da wannan (kyautar) daga waɗannan, ya ce: Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Shin ba za ku amince mini ba alhali ni ne amintaccen wanda ke sama, labarin sama yana zo mini safiya da yamma". Sai ya ce: Sai wani mutum ya miƙe idanuwansa sun shige cikin raminsu, kuma kundukukinsa ya fito, mai babban goshi, kuma gemunsa mai kaurine ba mai tsawo ba ne, mai askakken kai, yana janye da zaninsa wanda yake rufe ƙasan jikinsa da shi, sai ya ce: Ya Manzon Allah ka ji tsoron Allah, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Kaiconka, shin ba ni ne mafi cancantar mutanen dake doron ƙasa da jin tsoron Allah ba?!» Ya ce: Sannan mutumin ya juya baya, Khali ɗan Walid ya ce: Ya Maonzon Allah, shin ba na daki wuyansa ba? Ya ce: A'a, wataƙila yana sallah, sai Khalid ya ce: Da yawa mai sallar da yake faɗa da harshensa abinda babu shi a cikin zuciyarsa, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai cewa ni ba'a umarceni in bibiyi zukatan mutane ba ko in tsaga cikinsu ba; kaɗai an umarcenine in yi hukunci da zahirin al'amuransu, ya ce: Sannan ya kalle shi a lokacin ya juya baya, sai ya ce: Lallai wasu mutane zasu fito daga tsatson wannan da sahabbansa ko ƙabilarsa masu yawan hazaƙa a karatun Littafin Allah da murya mai daɗi, harsunansu ɗanyu ne saboda yawan karanta shi, Alƙur'ani ba zai wuce maƙogwaransu ba, sai zukatansu su kiyaye shi sai su gyara shi, kuma Allah ba Zai ɗaga shi (gareShi) ba kuma ba zai karɓe shi ba, zasu fita daga Musulunci kamar yadda kibiya take fita daga baka da aka harba da sauri kuma a ɓoye. Kuma ina zatansa ya ce: Wallahi idan na riski tawayensu akan musulmai da takobi zan yaƙesu yaƙi mai tsanani kamar mutanen Samudawa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Swahili Yaran Tailand Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Juriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma haƙurinsa akan cutarwa.
  2. Tabbatar da Annabcin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma lallai cewa abinda aka bashi wahayi ne.
  3. Yin mu'amala da mutane da abinda ya bayyana daga garesu, kuma Allah Yana jiɓintar abubuwan da suka ɓoye.
  4. Girmama matsayin sallah, kuma masu yin sallah ba'a kashesu sai da haƙƙin Musulunci.
  5. Haɗarin Kawarijawa, kuma cewa idan sun fito yaƙi to an shara'anta yaƙarsu dan kare cutarsu.
  6. Nawawi ya ce: Kwaɗaitarwa akan yaƙarsu da kuma falalar Aliyu - Allah Ya yarda da shi - a cikin yaƙarsu.
  7. Muhimmancin Tadabburi a ma'anonin Alƙur'ani da fahimtarsa da kuma aiki da shi da yin riƙo da shi.