عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: سمعتُ رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «ما مِن بَني آدم مَوْلودٌ إلا يَمَسُّه الشيطانُ حِين يُولَد، فيَسْتَهِلُّ صارخا مِن مَسِّ الشيطان، غير مريم وابنها» ثم يقول أبو هريرة: {وإنِّي أُعِيذُها بك وذُرِّيَّتَها من الشَّيطان الرَّجِيمِ}.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An kavo daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce naji Manzon Allah SAW yana cewa: "Babu wani da za'a haifa a cikin "yan Adam face sai Shaioxan ya shafeshi lokacin da za'a haife shi, sai ya faxo yana kuka daga shafar shaixan sai Maryam kawai da Xanta"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Kowane Jariri ana haifar sa sai Shaixan zai sokeshi a kuivinsa, sai ya kwalla kuka yayi Ihu bayan haihuwarsa kaxan saboda wannan zungurin na Shaxan, sai Maryam da Xanta Isa -Amincin Allah a garesu- saboda Allah ya kare su a lokacin haihuwarsu saboda Addu'ar Mahaifiyar Maryam lokacin da ta ce: "Kuma ni ina ne mata tsari da Zuriyarta daga Shaixan tsinanne" sai Allah ya amsa Addu'ar Mahaifiyar Maryam, sai ya kare Maryam da Xanta Isa daga zungurar Shaixan korarre ga barin rahamar Allah, Kuma babu wata Zariya ga Maryam in ba Isa -Amincin Allah a gare shi- kuma wannan Shafar ko sukar daga shaxan na haqiqa ne, kuma ba wai Ma'anarsa Kwaxayin Shaixan ba ne na vatar Xan Adam ba Kamar yadda Mu'atazilawa suke faxa, kuma ya wajaba ayi imani da hakan kan Haqiqaninsa, kamar yadda haka yake a Aqidar Ahlussunnah da jama'a

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Kurdawa
Manufofin Fassarorin