عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما «أن مُعَاذَ بْنَ جَبَل: كان يُصَلِّي مع رسول الله صلى الله عليه وسلم العِشاء الآخرة، ثم يرجع إلى قومه، فيُصَلِّي بهم تلك الصلاة ...». وفي رواية: أن النبي صلى الله عليه وسلم قال لِمُعَاذٍ: «فلولا صَلَّيْتَ بِسَبِّحِ اسم ربك الأعلى، والشمس وَضُحَاهَا، والليل إذا يغشى، فإنه يُصَلِّي وراءك الكبير والضعيف وذو الحاجة».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Jabir Dan Abdullahi "cewa Mu'az Dan Jabal ya kasance yana Sallah tare da Annabi Isha, Sannan ya dawo wajen Mutanensa, sannan yayi musu Sallah" "Mai ya hana kayi Sallah da Sabbi, da kuma washamsi, ko kuma Wallaili? sabida a bayanka cikin masu binka akwai Tsoho da rarrauna da mai bukata"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Gidajen Bani salama sun kasance, Mutanen Mu'az Dan Jabal Al'ansari a gefen Madina, kuma Mu'az ya kasance mai tsananin kwadayin Alkairi, sabida haka ya kasance mai kokarin Sallah tare da Annabi; sabida sonsa da Annabi da Annabi da kuma kwadayinsa da Ilimi, sannan bayan ya bada farillar sa bayan Annabi yakan jewa Mutanensa, kuma yayi musu Sallah, sai wannan sallar ta zamar Masa Nafila, Farilla kuma ga Mutanensa, kuma ya kasance hakan da sanin Annabi, kuma ya tabbatar masa da hakan, sai dai cewa shi yana tsawaita karatu kuma Shariar Musulunci ansanta da sauki da kuma rangwame, da rashin tsanantawa, domin tsanantawar da Matsantawar daga cikin aibinsa shi ne korar Mutanen yake, kuma yayin da hakan ya isarwa Annabin cewa Mu'az yana tsawaita karatun sai ya shiryar da shi izuwa sauki tunda dai shi ne limami, kuma ya nuna masa misalin ayoyin da zai karanta matsakaici kuma wanda yafi kamar sabbi, washamsi, da kuma Wallaili, domin cewa Manayn Mutane suna bin sallarsa, da kuma raunana, da Ma'abota bukatu wadanda dadewa zai matsanta musu, sabida haka ya dace a saukaka musu, kuma a kula da su ta hanayar saukakawa, amma idan ya kasance Musulmi yana Sallah shi kadai, to yana da damar yayi ta tsawaitawarsa yadda ya so.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin