عن أبي يحيى خُرَيْم بن فَاتِك رضي الله عنه مرفوعاً: «مَنْ أَنْفَقَ نَفَقَةً في سَبِيل الله كُتب له سَبْعُمِائَةِ ضِعْفٍ».  
                        
[صحيح] - [رواه الترمذي والنسائي وأحمد]
                        
 المزيــد ... 
                    
An rawaito daga Abu YahayaBin Khuzaim Bn Fatik -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Duk wanda ya ciyar a tafarkin Allah za'a rubuta masa ninkin Lada sau dari bakwai." 
                                                     
                                                                                                    
[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]                                            
Duk wanda ya ciyar da kadan ko wani abu mai yawa a kan tafarkin Allah Madaukakin Sarki, walau na jihadi ne saboda Allah - Madaukaki - ko kuma a wasu bangarorin na adalci da biyayya, Allah zai ninka ladarsa a Ranar Kiyama har sau dari bakwai.