«وَيْلٌ لِلْأَعْقَابِ مِنَ النَّارِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 242]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira da Abdullahi Dan Amru da A'isha - Allah ya yarda dasu - daga Manzo tsira da aminci su tabbata a gare shi - yace" Azabar wuta ta tabbata ga duga - dugai,
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi - Buhari da Muslim suka rawaito shi da ruwayoyin sa]
Annabi tsira da amincin Allah yana tsoratar da al'umma game da yin wasa da lamarin alwala da kuma gaza yin ta cikakkiya, ya kuma kwadaitar da a irika yinta cikakkiya, kasncewar an fi samun lam'a a duga - dugai, ruwa baya mamaye su sosai, wanda hakan ka iya jawo matsala ga tsarki da salla, sai Annabi ya bamu labarin azaba mai tsanani ga duga - dugai da kuma mai duga- dugan mai yin wasa da alwala