+ -

عن أَنَس بنِ مَالِكٍ رضي الله عنه «أنَّ جَدَّتَهُ مُلَيكَة دَعَت رسول الله صلى الله عليه وسلم لِطَعَام صَنَعتُه، فَأَكَل مِنه، ثم قال: قُومُوا فَلِأُصَلِّي لَكُم؟ قال أنس: فَقُمتُ إِلَى حَصِيرٍ لَنَا قد اسوَدَّ من طُولِ مَا لُبِس، فَنَضَحتُه بماء، فقام عليه رسول الله صلى الله عليه وسلم وَصَفَفتُ أنا واليَتِيمُ وَرَاءَهُ، والعَجُوزُ مِن وَرَائِنَا، فَصَلَّى لَنَا رَكعَتَين، ثُمَّ انصَرَف». ولمسلم «أن رسول الله صلى الله عليه وسلم صلى به وبِأُمِّه فَأَقَامَنِي عن يَمِينِه، وأقام المَرأةَ خَلْفَنَا».
[صحيح] - [الرواية الأولى: متفق عليها. والرواية الثانية: رواها مسلم]
المزيــد ...

An karbo daga Anas Dan Malik Allah ya yarda dashi"Cewa Kakarsa Mulaika ta gaiyaci Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi saboda wani Abinci da ta shirya masa,sai yaci daga gareshi.sannan yace:ku tashi nai muku Salla?sai Anas yace:Sai na tashi zuwa wata Tabarmarmu wace tayi Kura saboda an dade da shinfida ta,sai na yayyafa mata Ruwa,sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya tsaya akanta ni da Marayan sai muka yi sahu a bayansa,Tsohuwar kuma tana daga bayanmu, sai yayi mana Salla raka'a Biyu sannan ya juya".Daga Muslim kuma"Cewa Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi masa Salla da Mahaifiyarsa sai ya tsayar dani a Damansa,ya tsayar da Macen a bayanmu".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Mulaika Allah ya yarda da ita ta gaiyaci Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi saboda wani Abinci da ta shirya masa,hakika Allah Madaukakin Sarki ya halicceshi abisa mafi Girman Karamci kuma mafi Daukakar Dabi'u,yana daga cikinta Kaskantar da Kai mai yawa,ya kasance duk da daukakar Kadarinsa da kuma girman Matsayinsa yana amsa gaiyatar Babba da Karami,da Namiji da Mace,da Mawadaci da Talaka,yana nufi da hakan Manufofi Madaukaka, da kudure-kudure masu girma na daga gyara zukatan Mabukata,da kaskantar da kai ga Miskinai,da kuma sanarda Jahilai,da wasun wadannan na daga manufofinsa ababan yabo,sai yazo wajan wannan mai Gaiyatar,yaci daga Abincinta,sannan yayi amfani da wannan damar don ya sanar da wadannan Raunanan wadanda da yawa ba zasu iya gogayya da Manyaba a Mazauninsa mai Al-Barka,sai ya umarcesu da tsayawa don yayi musu Salla,kuma su san yadda ake yin Salla daga gareshi,sai Anas ya nufi wata tsohuwar Tabarma,wacce tayi kura saboda tsahon zama da amfani,sai ya wanke ta,sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya tsaya yana yi musu Salla,sai Anas yayi sahu,da wani Maraya dake tare dashi,sahu Daya bayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi,sai tsohuwar-maiGaiyatar-tayi sahu a bayan Anas da Marayan,tana Salla tare dasu,sai yayi musu Salla raka'a Biyu,sannan ya juya bayan ya cika hakkin Gaiyatar da kuma ilmantarwa tsira da amincin Allah su tabbata agareshi,Allah yayi mana baiwa ta binsa cikin Aiyukansa da Dabi'unsa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin