عن ابن عباس رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «لا يَنْبغي لِعَبْدٍ أنْ يقول: أنا خيرٌ مِن يونس بن مَتَّى» ونسبه إلى أبيه.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

Daga Ibn Abbas -Allah ya yarda da su- daga manzon Allah SAW ya ce: "Bai dace ga Bawa ba ya ce: Ni nafi Yunus Bin Matta" kuma nasabarsa zuwa Babansa ce
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Bai dace ga wani Muyum ba ya ce: cewa shi ya fi Yunusa Bn Matta -Amincin Allah a gare su- kuma Matta shi ne Babansa ba sunan Mahaifiyarsa ba ne, kuma yunus Annabin Allah ne mai girma daga cikin Annabawan Allah waxanda suka zo da Shiriya da Haske, don futar da Muatane daga Duhu kuma Annabi SAW ya ce: haka ne saboda qanqan da kai; saboda ya na daga cikin abunda aka sani ne cewa shi Manzon Allah SAW shi ne mafifitan Yayan Adam kuma cewa shi ya fadi hakan ne kafin yasan cewa shi ne mafificin Mutane, Kuma ya kevan Yunusa da wannan Maganar saboda abunda yake ji na qissarsa da ta faru yana yauye masa Daraja, Sai manzon Allah ya kambama shi cikin faxar falalar sa saboda yoshe qofar varna, kuma haqiqa Suddi ya rawaito qissarsa daga Ibn Masud da waninsa, cewa Allah ya tura Yunus zuwa Mutanen Nainawa ita ce garin Mausil a yanzu sai suka qaryata shi sai akai musu lakatin Azaba a wani lokaci ayyananne, sai ya futa ya barsu cikin fushi da su, yayin da suka ga alamun hakan sai suka risina ga Allah kuma suka qanqan da kai sukai Imani sai Allah ya ji qansu kuma ya yaye musu Azaba sai Yunus ya tafi ya hau jirgin Ruwa sai akai Quri'a sau uku ta faxa kansa sai suka jefa cikin Ruwan sai kifi ya haxiye shi , sai ya yi Addua cikin Duhunnai cewa babu wani Ubangijin sai kai tsarki ya tabbata a gareka ni na kasance cikin azzalumai sai Allah ya amsa Masa kuma ya umarci kifin da ya amayar da shi a bakin kogi, kuma Allah ya tsiro masa da Bishiyar Kabewa tayi masa Inuwa

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Bosniyanci Rashanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur
Manufofin Fassarorin