عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما «أَنَّ رَسُولَ الله صلى الله عليه وسلم قَسَمَ فِي النَّفَلِ: لِلْفَرَسِ سَهْمَيْنِ، وَلِلرَّجُلِ سَهْمًا».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Umar Allah ya yarda dasu- "Manzon Allah ya raba ganimar yaki: Sai yaba doki kaso biyu, mutum kuma kaso daya"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Abdullahi Dan Umar -Allah ya yarda dasu- yana bada labarin cewa Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi- ya yi rabon ganimar yaki ya bawa doki kaso biyu, mutum kuma kaso daya, kuma alkur'ani yayi nuni da haka inda Allah Madaukaki ke cewa:[Ina rantsuwa da dawaki masu kai hari da asuba, sai su tayar da kura game da shi, sai su shi tsakanin makiya da ita kurar] {al'adiyat 3-5}. Wannan na nuni ga muhimmancin doki a fagen daga. Annabi tsira da amincin Allah yace: [ Akwai alheri ga makwankwadar doki har zuwab ranar kiyama]

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Portuguese Malayalam
Manufofin Fassarorin