+ -

عن أبُي أَيُوب الأنصَارِيّ رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «غَدْوَةٌ فِي سَبِيلِ الله، أَوْ رَوْحَةٌ: خَيْرٌ مِمَّا طَلَعَتْ عَلَيْهِ الشَّمْسُ وَغَرَبَتْ». عن أنس رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «غَدْوَةٌ فِي سَبِيلِ الله، أَوْ رَوْحَةٌ: خَيْرٌ مِنْ الدُّنْيَا وَمَا فِيهَا».
[صحيح] - [الأول: رواه مسلم. الثاني: متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Ayuba Al'ansary -Allah ya yarda dashi- zuwa ga Annabi: "Yin sammako ko yammaci don Allah shi ne mafi alheri: a cikin fitowar Rana da faduwarta". Daga Anas -Allah ya yarda dashi- zuwa ga Annabi: "Yin sammako ko yammaci don Allah: shi ne mafi alheri akan duniya da abin da ke cikinta".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Wadannan hadisai biyu suna nuna mana falalar yin jihadi don Allah koda kuwa dan kadan ne gwargwadon lokacin safiya ko na yamma, ballantana kuma lokaci mai yawa wanda cikinsa akwai tsananin hakuri da gwagwarmaya da abokan gaba, wannan shi ake nufi da yi don Allah, watau yakar kafirai. Kuma ya kamata asan cewa neman ilmin sharia shina bangare ne mai girma na jihadi don Allah, hakanan taimakon gaskiya, hakanan ruguza hujjojin zindikai arna turawa yanmishan masu yakar musulumci masu son gani bayansa shi ne mafi girma cikin jihadi a tafarkin Allah. Manufar jihadi, shi ne bayyana Musulunci da taimaka masa, kuma dakushe arna, yana daga jihadi mai girma. Ya Allah ka datar da Musulmi a wajen taimakawa addininsu, da daukaka kalmarka. Kai ne Makusanci Mai amsawa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam
Manufofin Fassarorin