عن أبي مسعود عُقبة بن عَمْرو الأنصاري البَدْري رضي الله عنه مرفوعاً: «إن الشمس والقمر آيتان من آيات الله، يُخَوِّفُ الله بهما عباده، وإنهما لا يَنْخَسِفَان لموت أحد من الناس، فإذا رأيتم منها شيئا فَصَلُّوا، وَادْعُوا حتى ينكشف ما بكم»
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Lallai Rana da Wata ayoyi ne daga cikin ayoyoin Allah, wanda yakan tsoratar da bayinsa da su, kuma lallai ba su kisifewa don mutuwar wani da ga cikin mutane- don haka in kun ga wani abu makamancin hakan to ku yi sallah, ku roki Allah har ya yaye muku
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Manzo mai tsira da aminci ya bayyana cewa Rana da Wata suna daga cikin ayoyin Allah masu nuni akan kudurar Allah da hikimarsa, canjawarsu daga asalin yadda suke baya faruwa don rayuwa ko mutuwar wasu manyan mutane kamar yadda mutanen jahiliyya suke kudurcewa,abubuwanda kan afku a duniya basu da tasiri a kansu. kisifewar Rana ko Wata kan faru ne saboda tsoratar da bayi, don zunubansu haka kuma don su sabunta tubansu, don kuma su koma zuwa ga Allah Madaukaki. Don haka Manzo ya shiryar akan a tashi ayi salla da addu'a har su sami waraka su yaye. lallai ga Allah sururruka da jujjuyawar al'amura suke

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Portuguese
Manufofin Fassarorin