عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه مرفوعاً: «لاَ يُتْمَ بَعْدَ احْتِلاَمٍ، وَلاَ صُمَاتَ يوم إلى الليل».
[صحيح] - [رواه أبو داود]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An rawaito daga Ali Bn Abi Dali -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Babu wani Sauran Maraici bayan Balaga, ko kuma hakurin wuni zuwa dare"
Ingantacce ne - Abu Daud Ya Rawaito shi

Bayani

Na farko: ba'a daukar Mutumin da ya balaga Maraya Na biyu: Sun kasance a lokacin Jahiliyya suna bautawa Allah -Mai girma da daukaka- da yin shiru, sai ya zauna wuni guda yayi shiru baya Magana har rana ta fadi, sai ya hana Musulmi yin hakan; saboda wannan yana hana yin Tasbihi da kuma Tahlili da Tahmidi da umarni da kyakkyawan aiki da kuma hani da Mummunan aiki, da Karatun Qur'ani da wanin hakan, kuma har walau yana daga cikin aikin Jahiliyya saboda haka aka hana hakan.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese
Manufofin Fassarorin