عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «مَا يَجِدُ الشَّهيد من مَسِّ القتل إلا كما يَجِدُ أَحَدُكُمْ من مَسِّ القَرْصَةِ».
[حسن] - [رواه الترمذي وابن ماجه والنسائي والدارمي وأحمد]
المزيــد ...
Babu abinda Shahidi yake samunsa (Na Zafi) sai kamar abunda dayanku yake ji idan Turuwa ta cije shiAn rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Babu abinda Shahidi yake samunsa (Na Zafi) sai kamar abunda dayanku yake ji idan Turuwa ta cije shi"
[Hasan ne] - [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi - Al-Darumi Ya Rawaito shi]
Ma'anar hadisin: cewa idan mutum ya yi shahada saboda Allah, to me ya same shi daga masifar kisa da hadisin Al-Darami: "Daga zafin kashewa" ba ya jin ta sai dai kamar yadda dayanmu yake ji daga zafin tururuwa. Ma'anar: cewa shahidi baya shan wahala ta mutuwa da buguwarsa, kamar yadda yake ga sauran mutane, amma dai abinda ya sameshi kuma yake shan wahala idan ya mutu shine abinda muke samu daga cizon tururuwa a cikin zafin da take haifarwa cikin saurin bacewarta, don haka baya jin sa, kuma wannan yana daga falalar Allah Madaukaki. A kan shahidi, don lokacin da ya ba da ransa saboda Allah Madaukaki, Allah ya sauƙaƙa kashe shi.