عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ كَانَ فِي سَفَرٍ فَصَلَّى الْعِشَاءَ الْآخِرَةَ فَقَرَأَ فِي إِحْدَى الرَّكْعَتَيْنِ بِـ التِّينِ وَالزَّيْتُونِ. وَفِي لَفْظٍ: فَمَا سَمِعْتُ أَحَدًا أَحْسَنَ صَوْتًا أَوْ قِرَاءَةً مِنْهُ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 7546]
المزيــد ...
Daga Bara'u Dan Azib -Allah ya yarda da su-Annabi -tsira da aminci- ya kasance a wata tafiya, sai ya yi sallar Issha'i, ya karanta Wattini a daya daga cikin raka'oi biyun sallar, ban taba jin wani mai adadin sauti , ko dadin karatu kamar shi ba"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Annabi -tsira da aminci- ya karanta Suratuttini a raka'ar farko ta sallar Issha'i; saboda halin tafiya, ita tafiya ana saukaka salla lura da wahalar tafiya, duk da kasancewar Annabi -tsra da aminci Matafiyi, bai bar abin da zai samar da nutsuwa da halarto da zuciya wajen jinsa ba, watau kyautata sauti lokacin karatun salla.