عن سَبْرة بن معبد الجهني رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «إذا صلى أحدكم، فليسْتَتِر لصلاته، ولو بسهم».
[صحيح] - [رواه أحمد]
المزيــد ...
Daga Samra Bn Ma'abad Al-Juhani -Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah SAW ya ce: "Idan xayanku zai yi sallah to ya stuce sallarsa, ko da da Kibiya ne"
[Ingantacce ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi]
Wannan Hadisin yana bayanin Mustahabbanci ga Mai sallah ya sanya Sutura a gabansa, kuma lallai cewa Suturar tana iya yiwuwa da komai da mai Sallah zai kafa shi a gabansa, koda kuwa gajere ne kamar kibiya, kuma a cikin wannan akwai Alamu na sauqin Shari'a da rangwamenta