عن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما قال: «بينما رجل واقف بِعَرَفَةَ، إذ وقع عن راحلته، فَوَقَصَتْهُ -أو قال: فَأوْقَصَتْهُ- فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : اغْسِلُوهُ بماء وسدر، وكَفِّنُوهُ في ثوبيه، ولا تُحَنِّطُوهُ، ولا تُخَمِّرُوا رأسه؛ فإنه يُبْعَثُ يوم القيامة مُلبِّياً».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

a yayin da wani mutum ke tsaye a filin arfa, kwatsam sai ya fado daga kan dabbar da yake kai, sai ta taka shi- ko kuma ya ce: ta kayar da shi sai manzon Allah ya mai tsira da aminchi ya ce: ku wankeshi da ruwa da kuma magarya, ku yimasa likkafani a cikin tufafin sa, kada ku saka masa turare ko kafur, kada ku lullube masa kan shi, domin shi za`a tashe shi a ranar alqiyama yana talbiyyah
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

a yayin da wani mutum daga cikin sahabbai ke tsaye a filin arfa akan dabbar sa a lokacin Hajjin ban kwana yana cikin kayan ihrami sai ya fado daga kanta, sai wuyan sa ya karye ya mutu, sai manzon Allah mai tsira da aminchi ya umurce su da suyi masa wanka kamar yadda akewa sauran mamata yan`uwansa, da ruwa, da magarya su yimasa likkafani a cikin kwarjallen sa da mayafin sa, wadanda ya daura harama da su tare da cewa yayi harama da Hajji da kuma alamu na aikin ibada da suke tare da shi, hakika manzon Allah mai tsira da aminchi ya hana su da su saka masa turare ko su rufe kan sa ya ambata musu hikimar da ke cikin yin haka, ita ce Allah zai tashe shi akan abinda ya mutu akai, shi ne yin talbiyya, wadda ita ce alamar mutum yana cikin aikin hajji

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin