مِنْ كُلِّ اللَّيْلِ قَدْ أَوْتَرَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ أَوَّلِ اللَّيْلِ، وَأَوْسَطِهِ، وَآخِرِهِ، فَانْتَهَى وِتْرُهُ إِلَى السَّحَرِ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 745]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha ya ce: "A kowane dare Annabi yana wutiri ko afarkon dare ko tsakiyarsa, ko karshensa, Kuma yakan tsaida Wutirinsa da Asuba"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Nana Aisha tana bada labari game da lokacin da Annabi ya kasance yake sallatar Wuturi a cikin Dare, kuma cewa bai takaita a wani lokaci daya ba a kowane lokaci na dare yana yin Wuturi, wani lokacin ma a farkonsa lokacin da zai Sallaci Isha da kuma ya sawwaka bayant, kuma wani lokacin a tsakiyar daren bayan wucewar daya bisa ukunsa na farko, wani lokacin kuma daga karshensa lokacin da biyu bisa ukunsa suka shude, har ya kasance karshen lokacin Dare.