kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu, sai ya yi mana wa'azi, wa'azi isasshe zukata suka ji tsoro daga gare shi, idanuwa suka zubar da hawaye daga gareshi, aka ce: Ya Manzon Allah ka yi mana wa'azin bankwana to ka yi mana alkawari. Sai ya ce: '@Na horeku da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne mutumin Habasha, za ku ga sabani mai tsanani a bayana, to na horeku da sunnata da sunnar Halifofina shiryayyu*, ku rike su da turamen hakoranku, na haneku da fararrun al'amura, domin cewa kowacce bidi'a bata ce".
عربي Turanci urdu