عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «احرِصْ على ما يَنْفَعُكَ، واستَعِنْ بالله ولا تَعْجَزَنَّ، وإن أصابك شيء فلا تقُلْ: لو أنني فعلت لكان كذا وكذا، ولكن قل: قَدَرُ الله، وما شاء فعل، فإن «لو» تفتح عمل الشيطان».
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Kayi kwadayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah kuma kada ka Gaza, kuma koda wani abun ya sameka kada ka ce: Da ace nayi kaza da kaza da hakan bata faru ba sai dai kace: haka Allah ya kaddara, cewa (da nayi) to ita ce mabudin aikin Shaidan"
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi]

Bayani

Yayin da Musulun ya zo yana kira izuwa gina kasa da kuma Al'umma da gyara Mutane sai Annabi ya Umarco kowane Musulmi da yin aiki tukuru da kuma neman na kansa, yana mai neman taimakon tabbatar hakan da taimakon Allah, yana mai nisantar gazawa da duk abinda zai jawo shi, kuma kada ya budewa kansa kofar zargi ko nadama idan abin neman ya kubuce masa; domin hakan zai kaishi ga fushi da raki, kuma kawai cewa shi zai fawwala Al'marinsa zuwa ga Allah, kuma yasan sanadiyar hakan da Kaddara da hukuncin Allah ne har ya zamo ya toshe kofa ga Shaidan, sai shaidan girgiza masa Imaninsada Allah da kuma Imani da Kaddara da Hukuncisa.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin