عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه مرفوعاً: «ثلاثة لهم أجران: رجل من أهل الكتاب آمن بنبيه، وآمن بمحمد، والعبد المملوك إذا أدى حق الله، وحق مواليه، ورجل كانت له أمة فأدبها فأحسن تأديبها، وعلمها فأحسن تعليمها، ثم أعتقها فتزوجها؛ فله أجران».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
An rawaito daga Abu Musa Al-ash'ary -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi "Mutane Uku suna da Lada biyu: wani Mutum daga cikin Ahlul-Kitab da yayi Imani da Annabinsa, kuma yayi Imani da Annabi Muhammad, da kuma Bawan da ya bada Hakkin Allah da Hakkin Mai gidansa, da Kuma Mutumin da ya ke da baiwa ya kyautata tarbiyantar da ita, kuma ya sanar da ita kuma ya kyautata Sanar da ita, sannan ya Yantata sannan kuma ya Aureta, to yana da lada biyu"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
A cikin wannan hadisin bayani kan falalar mutanen littafi wadanda suka yi imani da Musulunci zuwa ga bin bin addininsu da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Saboda ya tausaya mata ya sake ta, sannan kuma yana da wani lada idan ya aure ta, ya dakata kuma ya kare farjinta.