عن عائشة -رضي الله عنها-: "أن أم سلمة ذكرت لرسول الله -صلى الله عليه وسلم- كنيسة رأتها بأرض الحبشة وما فيها من الصور، فقال: أولئك إذا مات فيهم الرجل الصالح أو العبد الصالح بنوا على قبره مسجدا، وصوروا فيه تلك الصور، أولئك شرار الخلق عند الله".
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Nana Aisha -Allah ya yarda a ita- "Lallai cewa Ummu Salama ta fadawa Annabi Wata coci da ta gani a kasar Habasha da kuma abinda yake ciki na Hotuna, sai yace: wadan can Idan Mutumin Kirki ya mutu daga cikinsuko bawa nagari sai su gina Masallaci akan Kabarinsa, kuma saka wadan nan Hotunan a ciki; wadancan sune Mafi Sharrin halittu a wajen Alla".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Lallai cewa Ummu salama ta sifanta wa Annabi kuma a lokacin yana rashin lafiyar Mutuwarsa, abinda ta gani a wani wurin bauta na Hotuna Mutane, sai Annabi ya yi mata bayayin cewa dalilin da yasa aka saka wadan nan Hotunan shi ne wuce gona da Iri wajen girmama bayin Allah; wanda hakan ya Jawo gina Masallaci akan Kaburbura da kuma kafa Hotuna a cikinsu, sannan ya bayyana Hukuncin duk wanda ya aikata hakan da cewa sune Mafi sharrin Mutane; sabida sun hada tsakanin laifuffuka guda biyu wadan da su ne: Fitinar kaburbura da sanya su Masallatai, da kuma Fitinar Girmama gumaka da abinda zai mai dakai zuwa Shirka.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Uighur
Manufofin Fassarorin