عن عبد الله بن عَبَّاسٍ رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «أُمِرْتُ أن أَسْجُدَ على سَبْعَةِ أَعْظُمٍ: على الْجَبْهَةِ -وأشار بيده إلى أنفه- واليدين، والرُّكْبَتَيْنِ ، وأطراف القدمين».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda dasu yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "An umarce ni da yin sujjada akan gabbai bakwai: goshi- sai ya nuna hancinsa da hannu, da hannaye biyu da gwuiwoyi biyu, da 'yan yatsun kafafuwa biyu
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Allah Madaukaki ya umarci Annabinsa -tsira da aminci su tabbata a gare shi- da yin sujjada akan gabbai bakwai, sune mafi darajar gabban da ke jikn dan adam; don ya zama kaskantar da kansa da ibadarsa ga Allah yake yi, Annabi tsira da amincin Allah ya fade su a dunkule kuma ya bayyana su filla-fila don a rike su kuma a rika kwadayin aikata su. Na farko: goshi da hanci. Na biyu da Na uku: tafin hannaye biyu su taba kasa. Na hudu da Na biyar: Sune gwuiwoyi biyu. Na shida da Na bakwai: yatsun kafa su kalli Alkibla