عن أبي سعيد الخدري -رضي الله عنه- أنَّ رسول الله -صلى الله عليه وسلم- بَعَث بَعْثاً إلى بني لحيان من هُذَيل، فقال: «لِيَنْبَعِث مِن كُلِّ رَجُلَين أَحَدُهُما، والأَجْرُ بَينهُما».
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

Daga Abu Sa'id Alkhudri -Allah ya yarda da shi- Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika wa Bani Lahyan manzo daga Hudhel, sai ya ce: A aiko shi daga kowane mutum biyu, dayansu, da lada a tsakanin su.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi]

Bayani

Ya zo a cikin Hadisin Abu Sa'id Al-Khudri -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah SAW yai nufin aika Rundunar Yaki zuwa Bani Lihyan, kuma su ne mafi Shaharar Kabilun Huzail, Kuma Malamai sun hadu kan cewa Bani Lihyan sun Kasance a cikin wancan lokaci Kafirai ne, sai ya aika musu da Tawaga da zasu yake su (Sai ya ce) da waccan runduna (Sai Mutum daya daga kowane mutane biyu ya futa) yana nufin daga kowace Kabila rabin Adadinta, (Kuma ladan) ai baki dayan abun da aka samu na Mayaki da wanda bai je ba yana da Alkairi (a tsakanin su) saboda shi ne Ma'anar fadinsa a cikin Hadisin da yake kafinsa "Kuma waye a cikin ya baro Sallama a gidansa da kuma dukiyarsa da Alkairi? to yana da lada kwatankwacin rabin Ladan wanda ya futa" Ma'ana cewa Annabi SAW ya Umarce su da su futar da daya daga cikin su, wani dayan kuma su bar daya ya maye gurbin Mayaki a gidansa, sai ya zamnato yana da rabin ladansa; Saboda rabin ladan na biyun na Mayaki ne

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara
Manufofin Fassarorin