عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا كَبَّر في الصلاة، سَكَت هُنَيَّة قبل أن يقرأ، فقلت: يا رسول الله بِأبي أنت وأمِّي أَرَأَيْتَ سُكُوتَكَ بين التَّكبير والقِراءة، ما تقول؟ قال "أقول: اللّهُم بَاعِد بَيْنِي وبَيْنَ خَطاياي كما بَاعَدْت بين المَشْرِق والمِغرب، اللَّهم نَقِّنِيَ من خطاياي كما يُنَقَّى الثوب الأبيض من الدَّنَس، اللَّهم اغْسِلْنِي من خَطَاياي بالثَّلج والماء والبَرد".
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...
An samu daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- yace: Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce: kaasance idan ya yi kabbarar harrama sai ya yi shiru na wani dan lokaci gabanin fara karatun fatiha sai nace: Ya Manzon Allah, fansar Baba na da Baba ta, bani labarin shiru da kake yi tsakanin kabbarar harama da karatun fatiha: me kake cewa? sai yace: cewa nake: ya Ubangiji na ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda ka nesanta tsakanin mahuda rana da mafadarta Ya Ubangiji na ka tsaftace ni daga zunubaina kanmar yadda kake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Ubangiji na ka wanke ni daga zunubai na da ruwan kankara da kuma mai tsananin sanyi
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi]